Dalilan Faduwar Farashi:
Ragewa daga $105K: Bayan hauhawar farashin da ya kai $105,000, an samu faduwa zuwa $102,415, sakamakon sayar da riba kafin fitar da bayanan hauhawar farashin kayayyaki na Amurka (CPI).
Liquidations: Faduwar farashin ya haifar da asarar kusan dala miliyan 700 ga masu dogon matsayi (long positions).
Sauran Altcoins: Ethereum (ETH) ya fadi zuwa $2,450, yayin da wasu altcoins suka fadi har zuwa 7%.
📊 Matakan Da Ake Kallon Su:
Resistance: $104,780 – $106,000
Support: $101,500 – $102,000
💡 Shawarwari:
Scalpers: Ku kula da matakan $102,000 da $104,000 don samun damar shiga da fita cikin sauri.
Swing Traders: Ku jira tabbatar da karyewar resistance kafin shiga kasuwa.
Long-Term Holders: Ku lura da yanayin kasuwa kafin ƙara jari.
Ba shawarar kasuwanci bace kayi naka binciken Dan yankewa kanka hukunci,
Menene Cryptocurrency???
MAI TAMBAYA: MENENE CRYPTOCURRENCY...?
AMSA: Ka ƙaddara a ranka crypto wani kuɗi ne na intanet, kamar dai yadda kuɗin takadda yake, sai dai kawai shi banbancinci da kuɗin takadda shine shi a intanet yake. A maimakon kuɗin takadda da gwamnatin ƙasa ke da iko dashi, to shi crypto yana aiki ne akan wani tsarin intanet mai ƴanci wadda ake kira da "Blockchain".
Akan wannan tsarin intanet ɗin na Blockchain ake ajiye bayanan komai na kuɗin crypto, duk wanda ka turawa kuɗin crypto konya turo maka idan aka duba zaayga wannan bayanan akan intanet na Blockchain. Tsarin intanet na Blockchain yana da tsananin tsaro fiye da normal intanet da muke dashi.
Banbancin tsarin Intanet na Blockchain da kuma Normal Intanet da muke amfani dashi shine: Misali kamar facebook yana kan normal intanet da muke amfani dashi, dan haka duk wanda yake amfani da facebook toh facebook suna da cikakken iko dashi.
Toh da ace facebook akan tsarin intanet na Blockchain yake toh facebook basu da wani iko dakai. Wannan dalilin yasa ake wa tsarin intanet na Blockchain laƙabi da "Intanet Mai Ƴanci", kana da damar yin komai naka ba tare da tsangwama ba.
"Idan nace iko ina nufin: Facebook nada ikon rufe ma account naka, restriction dinsa, hanaka comments dss"
Toh su wannan kuɗin crypto ɗin akan tsarin intanet na Blockchain aka gina su, shiyasa suma ake musu laƙabi da "Kuɗi Masu Ƴanci". A maimakon yanzu idan kana da kuɗi a bankinka, toh bankin nada iko dakai, toh su kuɗin crypto idan ka mallake su ka mallaka kenan ba wanda ya isa dasu in ba kai ba.
MAI TAMBAYA: TAYAYA KUƊIN CRYPTO SUKA ZAMA KUƊI DA HAR KAKE IYA CHANZA SU KA KARƁI NAIRA....?
AMSA: Kana ji yanzu idan na kirkiri kuɗin crypto akan Blockchain, da farko zan fara bashi adadi. Misali na kirkiri coin ɗin mai suna $ORC, dana tashi kirkirar sa sai na kirkiri guda 1Million. Toh da farkon lokaci dana kirkiri sa ba komai bane shi illa numbobi.
Lokacin da nake so ya zama kuɗi akwai hanyoyi guda 3 zuwa 5 da ake bi ya zama kuɗi, na 5 ɗin shine wanda yafi rikitarwa:
1. Na farko akwai abinda ake cewa ICO (Initial Coin Offering) ko kuma ace IPO (Initial Public Offering). Shi yadda tsarin yake shine: Zan dauki wannan coin ɗin nawa dana kirkira guda 1million mai suna $ORC, sai na bawa jama'ar gari dama akan su zo su sayi coin ɗin. Wannan kuɗin da zasuyi amfani dashi gurin siyan coin ɗin, shine kuɗin da zai zama abinda ake kira Liquidity.
"Liquidity: kowanne kuɗin crypto na buƙatar shi, Liquidity shine yake baka damar idan kana da kuɗin crypto ka iya chanza shi a baka Dollar ko Naira. Toh wannan kuɗin da ake karba na ICO shi ake amfani dashi guri Liquidity"
MAI TAMBAYA: TOH DAN ALLAH KAFIN KA TAFI NA 2, INA SON KA FAƊA MINI SU WAƊANDA SUKA SAYI COIN ƊIN A "ICO" TAYAYA SUKE CIN RIBA, KO KAWAI SAKAWA SUKE SHIKENAN KUƊIN SU YA TAFI A WOFI..?
AMSA: Shi kuɗin crypto yana hawa da sauka ne, misali idan na sayi coin a ICO yana kan a ƙaddara ₦10, to yayin daya shigo kasuwa mutane suka fara siye da siyarwa dashi. Farashin sa zai iya tashi ya zama ₦50, kaga kenan naci riba ko.
2. Bayan ICO, abu na biyu akwai abinda muke kira da IEO "Initial Exchange Offering", shima dai kamar ICO yake. Sai dai shi a maimakon zuwa da zakayi ka sayi coin direct ta hannun masu coin ɗin, shi IEO a kasuwannin crypto akeyin sa irin su Binance, Kucoin, CoinEx, Bitget dss.
3. Akwai kuma IDO "Initial Dex Offering".
"A crypto akwai tsarin gurin siyayya guda biyu, na farko akwai CEX "Centralized Exchanges" su gurin siyayya ne na crypto da suke aiki kamar banki, sai kayi KYC kayi komai kafin ka fara amfani dasu. Akwai kuma DEX "Decentralized Exchanges" asalin tsarin crypto kenan, shi kuma ba abinda ake buƙata kawai budewa zakayi ka fara amfani dasu"
Toh IDO anayin sa ne a gurin musayar crypto na DEX, shima duk yana aiki ne irin yadda ICO da IEO suke.
4. Sai kuma IFO "Initial Farming Offering", shi kuma sani tsari ne da akeyi wanda za'a ce ka sayi wani coin da tuntuni yana kasuwar crypto ka ajiye sa, za'a dinga baka wannan sabon coin ɗin da bai shigo kasuwa ba kyauta.
5. Sai na ƙarshe sanda yafi kowanne ruɗarwa shine IAO "Initial Airdrop Offering". Shi kuma coin ɗin ake rabawa kyauta ga mutane, amma fa dabara ce da ake amfani da ita dan tara mutane. Misalin irin wannan tsarin, akwai mining da mukeyi.
Suna dabara su tara mutane ta hanyar alkawarin zasu basu coin ɗin su kyauta, sai su ce musu suyi wani aiki. Lokacin da wa'adi ya cika, dama a chan gefe guda akwai wasu manya masu kuɗin crypto da kasuwanni da zasu ga. Ai project kaza yana da mutane da yawa.
Dan haka sai su dauki kudinsu su saka a matsayin Liquidity a sa coin ɗin a kasuwa, su kuma sai a basu wani adadi na coin ɗin, misali coin ɗin guda miliyan daya ne, sai a basu dubu 500k. Sai ace to a hankula zuwa wani lokaci zasu siyar da coin ɗin da aka basu.
MAI TAMBAYA: TOH SU TAYAYA AKE SUKE MAYAR DA WANNAN MAHAUKATAN KUƊAƊEN DA SUKE SAWA AKE BAWA MUTANE FREE...?
AMSA: Na faɗa muku cewa kuɗin crypto hawa yake da sauka ko? Toh mutane sune suke zama sanadin hawan nan nashi da sauka, yayi da suka dinga siya toh farashi zai tashi yayin da sukayi ta siyarwa toh farashi zai sauka.
Toh karka manta coin ɗin da akayi mining dole yana da mutane bila'adadin da suka san shi, dan haka akwai mutanen da muke kira da Traders da kuma Holders a crypto. Da zarar sun samu labarin coin ɗin zasu fara saka kuɗi, hakan zai sa ya dinga tashi.
Ta yiwu an saka shi a ₦100 duk guda daya, toh bayan Traders da Holders sun fara siya sai kaji farashin ya dawo ₦800. Su kuma wannan manyan masu kuɗin crypto da kasuwannin dama an basu guda dubu 500k, kamar yadda aka musu alkawari.
Sune suka saka masa kuɗi ya fito a farashin ₦100, kaga kenan idan suka siya a ₦100, sai dai ma su faɗi basu ci riba ba. Amma da sun tsaya yaje farashin ₦800, toh yanzu ya ninka musu kuɗin su x7. Kaga suna cikin riba.
Akwai coins da yawa a kasuwar crypto, yanzu haka akwai guda sama da dubu 30k. Dan haka babban abinda kowanne project na crypto suke nema shine a sansu, ba kuma za'a san su ba sai mutane sun san su. Hakane yasa suke neman mutane suyi mining ko task.
Yin wannan mining ɗin da task ne yake sawa duniyar crypto ta san project din, tunda maybe dubbunai ko miliyoyin mutane ke mining ɗin ko task. Dan haka da zarar ya fito, Traders da Holders na crypto suke fara siyansa. Wannan ke sawa farashin sa ya tashi.
Wallahu Ya'alamu....!

BARKA DA SAFIYA
Ilimin DAO A Sauƙaƙe
Ilimin DAO a sauƙaƙe cikin harshen Hausa.
Shin menene DAO?
Na sani da dama mutane ba su san me ake nufi da kalmar DAO, saboda ƙarancin fahimtar harshen Turanci da wasunmu suke samun matsala. Sannan kuma a wannan sahar mafi yawanci kaso 30% Hausawa ne suke cinikin kirifto.
To idan ko haka ne, malam wannan karatun naka ne don ka inganta hanyoyinka.
Ma'anar DAO a sauƙaƙe yana nufin "Kungiya mai cin gashin kanta wacce take aiki ta hanyar dijital". An samo kalmar daga Turanci:
Decentralized
Autonomous
Organization.
DAO wata kungiya ce da take amfani da smart contracts (kwangilolin wayo) a kan blockchain, inda babu shugaba guda ɗaya. Maimakon haka, mambobin kungiya ne ke yanke shawara ta hanyar zaɓe da ra’ayinsu.
Yadda DAO ke aiki a sauƙaƙe.
1. An tsara doka ta atomatik: A farkon kafa DAO, ana rubuta dokokinta a cikin smart contract. Wannan yana bayyana yadda ake zaɓe, yadda ake kashe kuɗi, da sauran dokoki.
2. Duk wanda ke da token na DAO:
Yana da iko da damar yanke shawarar yadda zai gudanar da abin shi.
Zai iya kaɗa kuri’a akan ƙuduri ko shawarar da za a aiwatar.
3. Zaɓe akan ƙuduri: Idan akwai sabon ƙuduri (misali, "mu zuba jari a wani sabon aiki"), mambobi za su kaɗa kuri’a. Idan yawancin ƙuri’un sun amince, tsarin zai aiwatar da wannan ƙuduri kai tsaye – ba tare da wani mutum ko shugaba ya sa hannu ba.
Amfanin DAO Ga Mutane masu buƙatar ilimin Web3.
Gaskiya da buɗaɗɗen aiki – komai a bayyane yake a kan blockchain.
Babu shugabanci na danniya – duka mambobi suna da haƙƙi iri ɗaya.
Sauƙin shiga – zaka iya shiga ta hanyar siyan token ɗinta.
Ikon jama’a – mambobi ke tsara shugabanci da ci gaban ƙungiya.
Misalan DAO
1. Uniswap DAO – wanda ke kula da musayar kuɗin crypto kai tsaye.
2. MakerDAO – da ke da alhakin kuɗin DAO, stablecoin na Ethereum.
3. Aave DAO – da ke bayar da lamuni da aro a duniya ta hanyar crypto.
Kalubale a DAO
Wani lokaci yakan ɗauki lokaci kafin a cimma matsaya.
Akwai matsalar zaɓe idan mambobi ba sa yin aiki da gaskiya.
Idan smart contract ɗin ya samu kuskure, yana iya haifar da asarar kuɗi.
A takaice:
DAO wata sabuwar hanya ce ta shugabanci wacce ke amfani da blockchain domin bai wa jama’a iko da 'yanci su tafiyar da Ƙungiyarsu ba tare da shugabanci na gargajiya ba.
Na gode.

JiddaWasha88
2025/05/07 17:11
CINIKIN CRYPTO NA HANNUNKA!!
Makomar Cinikin Crypto yana Tattare da Kai!
Dalilin da ya sa na faɗi haka, ina so ku sani shi crypto wani matattara ne da mutane suke haɗuwa suke juya kuɗaɗensu domin samun kuɗin shiga wato riba, wanda a yanzu haka damar samun kuɗin yake hannunka, tare da kuma samun manyan damarmakin gaske.
1. Yanzu haka, sabbin damar samun riba a crypto ba kawai suna faruwa ne a cikin exchanges ba.
Suna faruwa ma akan blockchain kai tsaye — kuma ta hannunka.
Da sahar Bitget, kana ganin duk abin da ke motsi, yadda kasuwar take sama da ƙasa, kafin kasuwar ta yi ƙasa (viral)
2. Me ake nufi da Sahar Bitget? (Bitget Onchain)
Wani tsari ne da yake haɗa sabbin tokens, tsarin tacewa mai ƙarfi, da sauƙin ciniki a wuri guda.
Ba sai ka dinga lilo tsakanin dApps, block explorer da wallets ba.
Duk inda crypto ke tashi, za ka ga shi a farko.
3. Abin da Sahar Bitget (Bitget Onchain) ke yi:
Na’urar tana duba kowani blockchain a daƙiƙa 60 kacal cikin aminci kuma.
Tana lura da sabbin tokens da ke karɓuwa a kasuwa a kowace rana.
Tana tantance su da metrics kamar FDV, volume, da holders
Kana iya tacewa bisa chain, category, da sauransu
4. Sauƙi da Sauri:
Ba sai ka san private keys ko yarda da wallet permissions ba.
Kawai tap, ka sayi token, ka cigaba da hada hadarka.
Wannan ne sabon Web3 da saurin CEX, da 'yancin DeFi.
5. Tsaro Kamar Wuta:
Ka sayi tokens kai tsaye daga Spot account naka (USDT/USDC).
Babu buƙatar wallet, seed phrase ko extensions.
Bitget yana kula da cinikin kamar siyan token a cikin app na banki!
6. Gano Sabbin Tokens Da Sauri:
Hot Picks: tokens masu tashi yanzu
New Picks: sabbin da aka ƙaddamar
Za ka iya tacewa bisa FDV, volume, ko wallet holders
Idan whales na sayen token, za ka gan shi kai tsaye.
7. Yanzu muna goyon bayan:
Solana
BNB Chain
Base
Sauran blockchains suna zuwa!
8. AI na taimaka maka:
Bitget Onchain yana amfani da AI don:
Tace kasada
Nuna dama mai fa'ida
da taimaka maka wurin yanke shawara cikin sauri da hankali
9. Gaskiya Cikakke:
Kana ganin:
Liquidity
Market Cap
Holders
Live charts
Kuma akwai Bitget Index Score wanda ke ba da ra'ayi daga metrics daban-daban.
10. Yadda zaka fara:
Shiga Bitget App
Danna [Markets] → [Onchain]
Zaɓi token → Duba bayani → Danna [Buy]
Saka adadi → [Confirm] → Jira ciniki → Tabbatar tokens ɗinka
Kana so ka sayar? Sauƙi kamar haka!
11. Ƙarshe:
Cinikin crypto ba zai taɓa tsayawa ba.
Amma tare da Bitget Onchain, kai ne gaban gaba.
Yanzu fa’idarka ba kawai abin da ka sani ba ne — sai yadda kake sauri da kuma yadda kayan aikinka ke aiki.
Wannan ne makomar crypto a mahangar jiya, yau da kuma gobe. Wannan ne Bitget Onchain.
Ga link ɗin nan ka shiga domin gwadawa.
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
Link: bitget.com/on-chain
Mu haɗu a kashi na huɗu.
Na gode.
Nakamoto Gamesのソーシャルデータ
直近24時間では、Nakamoto Gamesのソーシャルメディアセンチメントスコアは3で、Nakamoto Gamesの価格トレンドに対するソーシャルメディアセンチメントは強気でした。全体的なNakamoto Gamesのソーシャルメディアスコアは0で、全暗号資産の中で53にランクされました。
LunarCrushによると、過去24時間で、暗号資産は合計1,058,120回ソーシャルメディア上で言及され、Nakamoto Gamesは0.03%の頻度比率で言及され、全暗号資産の中で88にランクされました。
過去24時間で、合計1,039人のユニークユーザーがNakamoto Gamesについて議論し、Nakamoto Gamesの言及は合計296件です。しかし、前の24時間と比較すると、ユニークユーザー数は減少で8%、言及総数は減少で23%増加しています。
X(Twitter)では、過去24時間に合計1件のNakamoto Gamesに言及したポストがありました。その中で、100%はNakamoto Gamesに強気、0%はNakamoto Gamesに弱気、0%はNakamoto Gamesに中立です。
Redditでは、過去24時間にNakamoto Gamesに言及した8件の投稿がありました。直近の24時間と比較して、Nakamoto Gamesの言及数が20%減少しました。
すべてのソーシャル概要
3